AMFANIN MAN ZAITUN GA DAN ADAM
。
ZAITUN DA MAN ZAITUN
Shidai zaitun itaci- yace mai albarka da kuma bada cikakkiyar lafiya a jikin dan Adam , kamar yadda muka sani cewa zaitun abune mai daraja, kamar yadda muka samu bayaninta acikin ALKUR'ANI MAI GIRMA_
_haka kuma kamar yadda aka samu daga hadisan *Manzon Allah (ﷺ)an karbo daga sayyadina umar yana cewa Manzon Allah (ﷺ)* yace kuyi abinci da man zaitun kuma Ku shafashi ajikinku, domin hakika shi yana daga acikin bishiya mai albarka._tirmizi ne ya ruwaito
DAGA CIKIN AIKIN ZAITUN
KARFIN MAZAKUTA--* Duk mutumin da ya samu kanshi a wannan hali, to ya samu garin habbatussauda ya dinga zubawa acikin ruwan danyan kwai sannan a Soya shi da man zaitun ya dinga ci. Kullum , insha Allah zai samu karfin mazakuta sosai_
Kada ka gaji duk wani magani da kagani ka gwada zaka dace insha Allah_
CIWON CIKI
Duk mutumin da yake ciwon ciki sai ya samu man zaitun kamar cikin cokali ya hada da garin habbatussauda ya cakuda ya sha safe da yamma._
_Yasamu kamar sati daya yana sha ko kina sha insha Allah_
CIWON KAI
Duk mutumin da yake ciwon Kai to sai ya samu man zaitun yana shafawa a kansa yana kuma shan cokali daya da safe da Rana da dare insha Allah zai samu lafiya._
CIWON HAKORI
duk mutumin da yake ciwon hakori sai ya samo ganya zaitun da ya'yan habbatussauda ya sakasu acikin garwashi ya buda bakinsa hayakin ya dinga shiga, insha Allah._
CIWON HANTA
duk mutumin da ya kamu da wannan ciwo sai ya dinga shan manzaitun cikin cokali daya da safe daya da Rana daya da dare._
.
CIWON DADASHI
Duk mutumin da yake ciwon dasashi sai ya samu man zaitun ya dinga wanke bakinsa da shi._
.
_*CIWON SUKARI--* duk mutumin da ya kamu da ciwon sikari to sai ya samu man zaitun da tsamiya yana hadawa yana sha kafin ya kwanta bacci insha Allah_
.
sirrin rike miji
0 Comments